Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun sanar da cewa, da ƙarfe 4:50 na sanyin safiyar Alhamis, sun kai hari kan sansanin sojin saman Amurka wanda akai anfani da shi wajen kai harin ga wani wuri kusa da filin jirgin saman Bandar Abbas.
Dakarun sun kuma tabbatar da cewa wannan martani "gargaɗi ne mai tsanani" ga Amurka cewa duk wani hari da za ta kai wa Iran "ba zai wuce ba tare da an mayar da martani ba", suna kuma gargadin cewa sake maimaita hare-haren zai fuskanci martani "mafi tsanani".
Sanarwar ta tabbatar da cewa "bangaren da ya fara zalunci ne ke da alhakin dukkan sakamakon da zai biyo baya".
Wannan yana faruwa ne a daidai lokacin da sojojin Kuwait suka tabbatar da cewa "tsaron sararin samaniya yana fuskantar hare-hare da rokoki da jirage marasa matuki".
A baya kuma, kamfanin dillancin labarai na "Reuters" ya ruwaito daga wani jami'in Amurka cewa "sojojin Amurka sun kai sabbin hare-hare a kan wani wurin soji na Iran a yankin mashigar Hurmuz", kuma sun "kakkabo wasu jiragen marasa matuki na Iran da su kai yi imanin cewa suna barazana ga sojojin Amurka", a cewarsa.
A halin da ake ciki, wata majiyar soji ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na "Tasnim" na Iran cewa, wani jirgin ruwan Amurka mai ɗaukar mai ya yi ƙoƙari da sanyin safiyar Alhamis ya tsallaka mashigar Hurmuz ta hanyar kashe na'urar radar da ke cikinsa, amma an tilasta masa tsayawa inda ya koma bayan da sojojin ruwa na Iran suka dauki matakin gaggawa kuma mai tsauri na bude masa wuta a cewar majiyar.
Majiyar ta kara da cewa, sojojin Amurka sun bude wuta a kan "tsagwaron ƙasa" da ke kewaye da birnin Bandar Abbas, a daidai lokacin da aka ji karar fashe-fashe a yankin, ba tare da an samu raunuka ko asarar dukiya ba.
…………………………………………..
Your Comment